Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 13:18-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Mutumin da ba zai koya ba, zai talauce ya sha kunya, amma wanda ya kasa kunne ga tsautawa za a girmama shi.

19. Abu mai kyau ne mutum ya sami biyan bukatarsa! Wawaye sukan ƙi barin mugunta.

20. Ka koya daga wurin masu hikima, za ka zama mai hikima. Yi abuta da wawaye, za ka kuwa lalace.

21. Wahala tana bin masu zunubi ko'ina, amma za a sāka wa adalai da kyawawan abubuwa.

22. Mutumin kirki zai sami dukiya, har ya bar wa jikokinsa, amma dukiyar masu zunubi za ta zama ta adalai.

23. Saurukan da ba a aikatawa, za su ba da isasshen abinci ga matalauci, amma mutane marasa gaskiya sukan hana albarka.

24. Idan ba ka horon ɗanka, ba ka ƙaunarsa ke nan, amma idan kana ƙaunarsa za ka riƙa kwaɓarsa.

25. Adalai suna da isasshen abinci, amma mugaye fama suke da yunwa ko yaushe.

Karanta cikakken babi K. Mag 13