Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 13:13-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Idan ka ƙi shawara mai kyau wahala kake nemar wa kanka, idan ka bi ta kuwa za ka zauna lafiya.

14. Koyarwar masu hikima maɓuɓɓugar rai ce, za ta taimake ka ka kuɓuta sa'ad da ranka yake cikin hatsari.

15. Basira takan sa a girmama ka, amma mutanen da ba za a iya amincewa da su ba, a kan hanyar hallaka suke.

16. Mutum mai hankali a ko yaushe yakan yi tunani kafin ya aikata, amma wawa yakan tallata jahilcinsa.

17. Manzanni marasa aminci sukan haddasa wahala, amma waɗanda suke amintattu sukan kawo salama.

18. Mutumin da ba zai koya ba, zai talauce ya sha kunya, amma wanda ya kasa kunne ga tsautawa za a girmama shi.

19. Abu mai kyau ne mutum ya sami biyan bukatarsa! Wawaye sukan ƙi barin mugunta.

20. Ka koya daga wurin masu hikima, za ka zama mai hikima. Yi abuta da wawaye, za ka kuwa lalace.

21. Wahala tana bin masu zunubi ko'ina, amma za a sāka wa adalai da kyawawan abubuwa.

22. Mutumin kirki zai sami dukiya, har ya bar wa jikokinsa, amma dukiyar masu zunubi za ta zama ta adalai.

23. Saurukan da ba a aikatawa, za su ba da isasshen abinci ga matalauci, amma mutane marasa gaskiya sukan hana albarka.

24. Idan ba ka horon ɗanka, ba ka ƙaunarsa ke nan, amma idan kana ƙaunarsa za ka riƙa kwaɓarsa.

Karanta cikakken babi K. Mag 13