Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 10:5-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Mutum mai hankali yakan tattara amfanin gona da kaka, amma abin kunya ne a yi barci a lokacin girbi.

6. Mutumin kirki yakan karɓi albarka, maganganun mugun kuwa sukan ɓoye mugun halinsa.

7. Tunawa da mutumin kirki albarka ce, amma nan da nan za a manta da mugaye.

8. Mutane masu hankali sukan bi shawarar kirki, masu maganar wauta kuwa za su lalace.

9. Amintaccen mutum zai zauna lafiya ba abin da zai same shi, amma marasa aminci za a kama su.

10. Mutumin da ya ƙi faɗar gaskiya yana haddasa wahala, amma wanda ya bayyana gaskiya zai kawo salama.

11. Kalmomin mutumin kirki maɓuɓɓugan rai ne, amma kalmar mugun takan ɓoye makircinsa.

12. Ƙiyayya takan haddasa wahala, amma ƙauna takan ƙyale dukan laifofi.

13. Mutane masu fasaha sukan yi magana mai ma'ana, amma wawaye suna bukatar horo.

14. Mutane masu hikima sukan nemi ilimi iyakar iyawarsu, amma sa'ad da wawa ya yi magana, wahala tana kusa.

15. Wadata takan kiyaye attajiri, amma tsiya takan hallaka matalauci.

16. Sakayyar da za a yi wa mutumin kirki ta rai ce, amma zunubi yakan sa a ƙara yin wani zunubi.

17. Mutumin da yake kasa kunne sa'ad da ake kwaɓarsa zai rayu, amma duk wanda bai yarda da kuskurensa ba yana cikin hatsari.

Karanta cikakken babi K. Mag 10