Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 10:26-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Sam, kada ka sa malalaci ya yi maka wani abu, zai sa ka ka yi fushi, idanunka su cika da hawaye mai zafi.

27. Ka yi tsoron Ubangiji za ka rayu, ka yi tsawon rai, amma mugaye sukan mutu tun kwanansu bai ƙare ba.

28. Abin da mutanen kirki suke sa zuciya yakan kai su ga murna, amma mugaye ba su da wani abu da za su sa zuciya a kai.

29. Ubangiji yana kiyaye marasa laifi, amma yakan hallaka masu mugunta.

30. Kullayaumi adalai sukan yi zamansu lafiya, amma mugaye ba za su zauna a ƙasar ba.

31. Maganar adalai ta hikima ce, amma harshen da yake hurta mugunta, za a dakatar da shi.

32. Adalai sun san irin maganar da ta cancanta su faɗa, amma mugaye, kullum sukan faɗi maganar da za ta cutar.

Karanta cikakken babi K. Mag 10