Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 10:15-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Wadata takan kiyaye attajiri, amma tsiya takan hallaka matalauci.

16. Sakayyar da za a yi wa mutumin kirki ta rai ce, amma zunubi yakan sa a ƙara yin wani zunubi.

17. Mutumin da yake kasa kunne sa'ad da ake kwaɓarsa zai rayu, amma duk wanda bai yarda da kuskurensa ba yana cikin hatsari.

18. Mutumin da yake faɗar ƙarairayi maƙiyi ne, dukan wanda yake baza jitajita wawa ne.

19. Bisa ga yawan surutunka, mai yiwuwa ne ƙwarai ka yi zunubi, amma idan kai mai la'akari ne, sai ka yi shiru.

20. Kalmomin mutumin kirki suna kama da azurfa tsantsa, amma shawarwarin mugu ba su da wani amfani.

21. Kalmomin mutumin kirki za su amfani mutane da yawa, amma kana iya hallaka kanka da wauta.

22. Albarkar Ubangiji takan arzuta mutum, amma yawan aiki ba shi yake kawo arziki ba.

23. Wawa ne yake jin daɗin aikata mugunta, amma mai fasaha yana jin daɗin hikima.

24. Abin da mugun yake tsoro, shi yakan auko masa, amma adali yakan sami biyan bukatarsa.

Karanta cikakken babi K. Mag 10