Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 1:5-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Waɗannan karin magana sukan ƙara wa masu ilimi hikima, sukan zama jagora ga masana,

6. don su fahimci ɓoyayyiyar ma'anar da take cikin karin magana, da mawuyatan al'amura waɗanda masu hikima suka ƙago.

7. In kana so ilimi dole ne ka fara da tsoron Ubangiji. Jahilai ba su san darajar hikima ba, sun kuwa ƙi su koya.

8. Ɗana, ka kasa kunne ga koyarwar mahaifinka, ka mai da hankali ga abin da mahaifiyarka take faɗa.

9. Koyarwarsu za ta inganta halinka, ta zama kayan ado kamar kyakkyawan rawani a kanka, ko kyakkyawan abin wuya a wuyanka, don su ƙara maka kyau.

10. Ɗana sa'ad da masu zunubi suka jarabce ka, kada ka yarda

11. in suka ce maka, “Zo mu tafi mu nemi wani mutum mu kashe, mu je, mu fāɗa wa marasa laifi mu ji daɗi!

12. Ba mu damu da ransu da lafiyarsu ba, mu dai mu tafi mu kashe su, mu hallaka su ɗungum.

13. Za mu sami dukiya iri iri, mu cika gidajenmu da ganima!

14. Ka zo ka haɗa kai da mu, dukanmu kuwa za mu raba abin da muka sato.”

15. Ɗana, kada ka gama kanka da irin waɗannan mutane, ka yi nesa da su.

16. Ba su kasalar aikata mugunta, kullum a shirye suke su yi kisankai.

17. Ba shi da amfani a kafa tarko a idon tsuntsun da ake so a kama.

18. Amma waɗannan irin mutane kansu suke kafa wa tarko. Ba za su kama kome ba, sai rayukansu.

19. Yin fashi yakan zama sanadin mutuwar ɗan fashi a koyaushe. Wannan shi ne abin da yakan sami kowane mutum da ya kama sana'ar sata.

Karanta cikakken babi K. Mag 1