Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 1:26-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Saboda haka, lokacin da kuke shan wahala, zan yi muku dariya. Zan yi muku ba'a lokacin da razana ta auka muku,

27. sa'ad da ta zo muku kamar hadiri mai ƙaƙƙarfar iska mai wahalarwa, sa'ad da kuke shan azaba da damuwa.

28. Sa'an nan za ku kira gare ni, amma ba za ku same ni ba. Za ku neme ni a ko'ina, amma ba za ku same ni ba.

29. Domin ba ku taɓa sanin amfanin ilimi ba, kun ƙi tsoron Ubangiji a kullum.

30. Ba ku taɓa yarda da shawarata ba, ko ku yarda in gyara kuskurenku.

31. Saboda haka za ku karɓi sakayyarku, ayyukanku za su cuce ku.

32. Marasa sani sukan mutu saboda ba su yarda da hikima ba. Wawaye kuwa sukan hallaka saboda rashin kulawarsu.

33. Amma duk wanda ya kasa kunne gare ni, zai zauna lafiya. Ba abin da zai same shi, ba abin da zai tsorata shi.”

Karanta cikakken babi K. Mag 1