Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 1:16-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Ba su kasalar aikata mugunta, kullum a shirye suke su yi kisankai.

17. Ba shi da amfani a kafa tarko a idon tsuntsun da ake so a kama.

18. Amma waɗannan irin mutane kansu suke kafa wa tarko. Ba za su kama kome ba, sai rayukansu.

19. Yin fashi yakan zama sanadin mutuwar ɗan fashi a koyaushe. Wannan shi ne abin da yakan sami kowane mutum da ya kama sana'ar sata.

20. Ku kasa kunne! Hikima tana kira a tituna da a kasuwoyi.

21. Tana kira da ƙarfi a ƙofofin birni, a duk inda mutane suke tattaruwa.

22. Ta ce, “Wawayen mutane! Har yaushe za ku yi ta kasancewa haka? Har yaushe za ku daina jin daɗin yi wa mai ilimi ba'a? Faufau ba za ku taɓa koya ba?

23. Ku kasa kunne lokacin da nake tsauta muku, zan ba ku shawara mai kyau, mu yi tarayya cikin ilimina.

24. Ina ta kiranku ina gayyatarku ku zo, amma ba ku kula ba, ba ku mai da hankali gare ni ba.

25. Kun ƙi bin shawarwarina duka, ba ku yarda in gyara kuskurenku ba.

26. Saboda haka, lokacin da kuke shan wahala, zan yi muku dariya. Zan yi muku ba'a lokacin da razana ta auka muku,

27. sa'ad da ta zo muku kamar hadiri mai ƙaƙƙarfar iska mai wahalarwa, sa'ad da kuke shan azaba da damuwa.

28. Sa'an nan za ku kira gare ni, amma ba za ku same ni ba. Za ku neme ni a ko'ina, amma ba za ku same ni ba.

29. Domin ba ku taɓa sanin amfanin ilimi ba, kun ƙi tsoron Ubangiji a kullum.

30. Ba ku taɓa yarda da shawarata ba, ko ku yarda in gyara kuskurenku.

31. Saboda haka za ku karɓi sakayyarku, ayyukanku za su cuce ku.

32. Marasa sani sukan mutu saboda ba su yarda da hikima ba. Wawaye kuwa sukan hallaka saboda rashin kulawarsu.

Karanta cikakken babi K. Mag 1