15. Joshuwa kuwa ya yi amana da su, ya yi musu alkawari zai bar su da rai. Shugabannin jama'a kuma suka rantse musu.
16. Amma a rana ta uku bayan da suka yi alkawari da su, suka ji cewa, su maĈwabtansu ne, suna zaune a cikinsu.
17. Sai Isra'ilawa suka kama hanyarsu a rana ta uku suka isa biranen mutanen, wato Gibeyon, da Kefira, da Biyerot, da Kiriyat-yeyarim.
18. Amma Isra'ilawa ba su kashe su ba, domin shugabannin jama'a sun rantse musu da sunan Ubangiji Allah na Isra'ila. Dukan jama'a kuwa suka yi gunaguni a kan shugabannin.