Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 14:4-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Jama'ar Yusufu kuwa kabila biyu ce, wato Manassa da Ifraimu. Ba a kuma ba Lawiyawa rabon gādo a ƙasar ba, sai dai an ba su biranen da za su zauna, da filayen da za su yi kiwon garkensu.

5. Jama'ar Isra'ila fa suka yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa, suka rarraba ƙasar ta hanyar kuri'a.

6. Mutanen Yahuza suka je wurin Joshuwa a Gilgal, sa'an nan Kalibu, ɗan Yefunne Bakenizze, ya ce masa, “Ka dai san maganar da Ubangiji ya yi wa Musa, mutumin Allah, a Kadesh-barneya a kaina.

7. Ina da shekara arba'in sa'ad da Musa bawan Ubangiji ya aike ni daga Kadesh-barneya don in leƙi asirin ƙasar. Na kuma kawo masa ainihin rahoton yadda yake a zuciyata.

8. Amma 'yan'uwana da muka tafi tare, sun karya zukatan jama'ar, amma ni na bi Ubangiji Allahna da aminci.

Karanta cikakken babi Josh 14