Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 14:12-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Saboda haka sai ka ba ni ƙasar tuddai da Ubangiji ya ambata a ranan nan, gama a wannan rana ka ji yadda gwarzaye suke a can da manyan birane masu garu, mai yiwuwa ne Ubangiji zai kasance tare da ni, in kore su kamar yadda Ubangiji ya faɗa.”

13. Joshuwa ya sa wa Kalibu, ɗan Yefunne, albarka. Ya ba shi Hebron ta zama gādonsa.

14. Domin haka Hebron ta zama gādon Kalibu, ɗan Yefunne Bakenizze, har wa yau, domin ya bi Ubangiji Allah na Isra'ila sosai.

15. A dā sunan Hebron Kiriyat-arba ne. Arba kuwa babban mutum ne cikin gwarzayen. Ƙasar kuwa ta shaƙata da yaƙi.

Karanta cikakken babi Josh 14