Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 66:19-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. su kuwa sani ni ne wanda yake hukunta musu.“Amma zan bar waɗansu, in aika da su ga al'ummai da manisantan ƙasashe inda ba a ji labarin sunan da na yi ba, ba a kuwa ga girmana da ikona ba, wato zuwa Tarshish, da Libiya, da Lidiya, duk da gwanayen maharbanta, Rosh da Tubal, da kuma Helas. Za su ba da labarin girmana ga waɗannan al'ummai.

20. Za su taho da 'yan ƙasarku daga al'ummai, su kawo mini su kyauta. Za su zo da su a tsattsarkan dutsena, wato Urushalima, za su kawo su a kan dawakai, da alfadarai, da raƙuma, da cikin karusai, kamar dai yadda Isra'ilawa suke kawo hadaya ta hatsi a Haikali cikin tsabtatattun ƙore.

21. Zan sa waɗansu su zama firistoci da Lawiyawa.”

22. Ubangiji ya ce, “Kamar yadda sabuwar duniya da sabon sararin sama za su tabbata ta wurin ikona, haka zuriyarku da sunanku za su tabbata.

23. A kowane bikin amaryar wata, da kowace ranar Asabar, jama'ar kowace al'umma za su zo su yi mini sujada a nan cikin Urushalima.

24. Sa'ad da suke tafiya, za su ga gawawwakin mutanen da suka yi mini tayarwa. Tsutsotsin da suke cinsu ba za su taɓa mutuwa ba, wutar da take ƙona su kuma ba za ta taɓa mutuwa ba. Dukan mutane za su ji ƙyamarsu.”

Karanta cikakken babi Ish 66