Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 57:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Adalin mutum yakan mutu, amma ba wanda ya kula. An kwashe mutanen kirki ba kuwa wanda ya kula, an tsame adali daga cikin bala'i.

2. Ya shiga da salama yana hutawa a kabarinsa, shi wanda ya yi tafiya da adalci.

3. Amma ku ku matso nan kusa, ku 'ya'ya maza na masu sihiri, ku zuriyar mazinaci da karuwa.

4. Wa kuke yi wa ba'a? Ga wa kuke wage baki, kuna zaro harshe? Ashe, ku ba 'ya'yan masu laifi ba ne, zuriyar marikita,

5. ku da muguwar sha'awa take ƙonawa a tsakanin itatuwan oak, da ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa. Ku da kuka karkashe 'ya'yanku a cikin kwaruruka, da a ƙarƙashin duwatsu masu tsayi?

Karanta cikakken babi Ish 57