Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 52:9-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ku ɓarke da sowar murna,Ku kufan Urushalima!Ubangiji ya ta'azantar da jama'arsa,Ya fanshi birninsa.

10. Ubangiji ya nuna ikonsa mai tsarki,Ya ceci jama'arsa,Dukan duniya kuwa ta gani.

11. Ku fita, ku bar BabilaKu dukanku da kuke ɗauke da keɓaɓɓen kayan Ubangiji!Kada ku taɓa abin da aka hana,Ku kiyaye kanku da tsarki,Ku fita ku bar birnin.

12. A wannan lokaci ba za ku bukaci ku fita da garaje ba,Ba za ku yi ƙoƙari ku tsere ba!Ubangiji Allah ne zai bishe ku,Ya kuma kiyaye ku ta kowane gefe.

13. Ubangiji ya ce,“Bawana zai yi nasara a aikinsa,Zai zama babba, a kuwa girmama shi ƙwarai.

14. Mutane da yawa suka gigice sa'ad da suka gan shi,Ya munana har ya fita kamannin mutum.

15. Amma yanzu al'ummai da yawa za su yi mamaki a kansa,Sarakuna kuwa za su riƙe baki saboda mamaki.Za su gani su kuma fahimci abin da ba su taɓa sani ba.”

Karanta cikakken babi Ish 52