Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 5:28-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Kibansu masu tsini ne, bakunansu kuwa a shirye suke don yin harbi. Kofaton dawakansu suna da ƙarfi kamar dutsen ƙanƙara, ƙafafun karusansu kamar guguwa ne.

29. Sojojinsu na ruri kamar zakunan da suka kashe nama, suna kuwa ɗauke da shi don kada wani ya ƙwace musu.

30. Sa'ad da ranar ta yi, za su yi ruri a kan Isra'ila da ƙarfi kamar rurin teku. Ku duba ƙasan nan! Duhu da damuwa! Duhu ya haɗiye hasken.

Karanta cikakken babi Ish 5