Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 5:16-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Amma Ubangiji Mai Runduna yana nuna girmansa ta wurin aikata abin da yake daidai, yana kuma bayyana shi Mai Tsarki ne, ta yadda yake shara'anta jama'arsa.

17. A cikin kangwayen birnin, raguna za su ci ciyawa, a nan ne kuma awaki za su sami wurin kiwo.

18. Kun shiga uku! Ba ku iya kuɓuta daga zunubanku ba.

19. Kukan ce, “Bari Ubangiji ya gaggauta ya aikata abin da ya ce zai yi don mu gani. Bari Allah, Mai Tsarki na Isra'ila, ya i da shirye-shiryensa. Bari mu ga abin da yake nufi.”

20. Kun shiga uku! Kun ce mugunta ita ce nagarta, nagarta kuwa mugunta. Kun mai da duhu shi ne haske, haske kuwa duhu. Kun mai da abin da yake mai ɗaci mai zaƙi, mai zaƙi kuwa kun maishe shi mai ɗaci.

21. Kun shiga uku! A tsammaninku ku masu hikima ne, masu wayo ƙwarai.

22. Kun shiga uku! Jarumawan kwalabar ruwan inabi! Masu ƙarfin zuciya marasa tsoro a gauraya shaye-shaye!

23. Amma kukan ƙyale masu laifi waɗanda suka ba ku rashawa, kukan kuwa ƙi yi wa marasa laifi shari'ar gaskiya.

24. Don haka, kamar yadda tattaka da busasshiyar ciyawa sukan yanƙwane su ƙone a wuta, saiwoyinku za su ruɓe, furanninku kuma za su bushe. Iska za ta kwashe su, domin kun ƙi abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya koya muku.

25. Ubangiji yana fushi da jama'arsa, ya miƙa hannunsa domin ya hukunta su. Duwatsu za su jijjigu, gawawwaki kuwa za a bar su a kan tituna kamar shara. Duk da haka Ubangiji ba zai huce daga fushinsa ba, ba kuwa zai janye hannunsa daga yin hukunci ba.

26. Ubangiji ya ba da alama a kirawo al'ummar da take nesa. Ya yi musu fīto su zo daga bangon duniya. Ga shi kuwa sun iso da sauri nan da nan.

27. Ko ɗaya ba wanda ya gaji, ba kuwa wanda ya yi tuntuɓe. Ba su yi gyangyaɗi ko barci ba. Ba abin ɗamarar da ya kwance, ba igiyar takalmin da ta tsinke.

Karanta cikakken babi Ish 5