Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 45:21-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Ku zo ku gabatar da matsalarku a ɗakin shari'a,Bari waɗanda aka kai ƙara su yi shawara da juna.Wane ne ya faɗi abin da zai faru,Ya kuma yi annabci tuntuni?Ashe, ba ni ba ne, Ubangiji, Allah wanda ya ceci mutanensa?Ba wani Allah sai ni.

22. “Ku juyo wurina a cece ku,Ku mutane ko'ina a duniya!Ni kaɗai ne Allah da yake akwai.

23. Abin da na faɗa gaskiya ne,Ba kuwa zai sāke ba.Ni, a dukkan yadda nake, na yi alkawari mai ƙarfi,Kowa da kowa zai zo ya durƙusa a gabana,Ya yi wa'adin zama mai biyayya a gare ni.

24. “Za su ce ta wurina kaɗaiZa a iya samun nasara da ƙarfi,Amma dukan waɗanda suka raina ni za su sha kunya.

25. Ni Ubangiji, zan kuɓutar da dukan zuriyar Yakubu,Za su kuwa yi yabona.”

Karanta cikakken babi Ish 45