Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 45:20-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Ubangiji ya ce,“Ku taru wuri ɗaya ku jama'ar al'ummai,Dukanku da kuka tsira daga faɗuwar mulki,Ku gabatar da kanku domin shari'a!Waɗancan da suka ɗauka gumakansu na itace,Suna kuma addu'a ga allolin da ba su iya cetonsu,Waɗannan mutane ba su san kome ba ko kaɗan!

21. Ku zo ku gabatar da matsalarku a ɗakin shari'a,Bari waɗanda aka kai ƙara su yi shawara da juna.Wane ne ya faɗi abin da zai faru,Ya kuma yi annabci tuntuni?Ashe, ba ni ba ne, Ubangiji, Allah wanda ya ceci mutanensa?Ba wani Allah sai ni.

22. “Ku juyo wurina a cece ku,Ku mutane ko'ina a duniya!Ni kaɗai ne Allah da yake akwai.

23. Abin da na faɗa gaskiya ne,Ba kuwa zai sāke ba.Ni, a dukkan yadda nake, na yi alkawari mai ƙarfi,Kowa da kowa zai zo ya durƙusa a gabana,Ya yi wa'adin zama mai biyayya a gare ni.

24. “Za su ce ta wurina kaɗaiZa a iya samun nasara da ƙarfi,Amma dukan waɗanda suka raina ni za su sha kunya.

Karanta cikakken babi Ish 45