Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 43:24-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Ba ku sayi turare domina ba,Ko ku gamshe ni da kitsen dabbobinku.Maimakon haka, sai kuka nawaita mini da zunubanku,Kuka gajiyar da ni da abubuwan da kuke aikatawa da ba daidai ba.

25. Duk da haka, ni ne Allah wanda ya shafe zunubanku,Na kuwa yi haka saboda yadda nake.Ba zan ƙara tunawa da zunubanku kuma ba.

26. “Bari mu tafi ɗakin shari'a, ku kawo ƙararrakinku.Ku gabatar da matsalarku don a tabbatar kuna da gaskiya!

27. Kakanninku na farko sun yi zunubi,Manyanku sun yi mini laifi.

28. Zan musunci masu mulkin tsattsarkan masujadai,Saboda haka zan jawo wa Isra'ila hallaka,Zan bari a la'anta mutanena su sha zagi!”

Karanta cikakken babi Ish 43