Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 42:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce,“Ga bawana, wanda na ƙarfafa,Wanda na zaɓa, wanda nake jin daɗinsa.Na cika shi da ikona,Zai kuwa kawo shari'ar gaskiya ga dukan al'ummai.

2. Ba zai yi tsawa ko ya ta da muryarsa ba,Ko ya yi jawabi da babbar murya a tituna.

3. Zai lallaɓi marasa ƙarfi,Ya nuna alheri ga tafkakku.Zai kawo madawwamiyar gaskiya ga duka.

4. Ba zai fid da zuciya ko ya karai ba,Zai kuma kafa gaskiya a duniya,Manisantan ƙasashe sun zaƙu, suna jiran koyarwarsa.”

5. Allah ya halicci sammai ya kuma shimfiɗa su,Ya yi duniya, da dukan masu rai nata,Ya ba da rai da numfashi ga dukan mutanenta.Yanzu kuwa Ubangiji Allah ya ce wa bawansa,

6. “Ni Ubangiji, na kira ka, na kuma ba ka ikoDomin ka ga ana aikata gaskiya a duniya.Ta wurinka zan yi wa dukan mutane alkawari,Ta wurinka zan kawo haske ga al'ummai.

7. Za ka buɗe idanun makafi,Ka kuma kwance waɗanda suke ɗaure a kurkuku masu duhu.

8. “Ni kaɗai ne Ubangiji Allahnka.Ba wani allahn da zai sami ɗaukakata,Ba zan bar gumaka su sami yabona ba.

9. Abubuwan da na faɗa yanzu sun cika.Yanzu zan faɗa muku sababbin abubuwa,Tun kafin ma su soma faruwa.”

10. Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji,Ku raira yabo ku dukan duniya!Ku yabe shi, ku da kuke tafiya ta teku,Ku yabe shi, ku dukan halitta a teku!Ku raira, ku manisantan ƙasashe, da dukan waɗanda suke a can!

Karanta cikakken babi Ish 42