Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 40:12-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Akwai wanda zai iya auna teku da tafin hannu,Ko sararin sama da tafin hannunsa?Akwai wanda zai iya tallabe turɓayar duniya a cikin finjali,Ko ya iya auna duwatsu da tuddai a ma'auni?

13. Akwai wanda zai iya umartar Ubangiji ya yi abu?Wa zai iya koya wa Ubangiji, ko ya yi masa shawara?

14. Da wa Allah yake yin shawaraDomin ya sani, ya kuma fahimta,Ya kuma koyi yadda za a yi abubuwa?

15. Al'ummai ba kome ba ne a wurin Ubangiji,Ba su fi ɗigon ruwa ba,Manisantan tsibirai ba su fi ƙura nauyi ba.

16. Dukan dabbobin da yake a jejin LebanonBa su isa hadaya guda ga Allahnmu ba,Itatuwan jejin kuma ba su isa a hura wuta da su ba.

17. Al'ummai ba kome ba ne ko kaɗan a gare shi.

18. Da wa za a iya kwatanta Allah?Wa zai iya faɗar yadda yake?

19. Shi ba kamar gunki yake ba, wanda mutane suka yi,Maƙera kuma suka dalaye da zinariya,Suka sa shi cikin abin da suka yi da azurfa.

Karanta cikakken babi Ish 40