Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 40:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce,“Ka ta'azantar da jama'ata.Ka ta'azantar da su!

2. Ka ƙarfafa jama'ar Urushalima.Ka faɗa musu sun sha wahala, ta isa,Yanzu kuwa an gafarta musu zunubansu.Na yi musu cikakken hukunci saboda dukan zunubansu.”

3. Murya tana kira tana cewa,“Ka shirya hanya a jeji domin Ubangiji!Ka share hanya a hamada domin Allahnmu!

4. Za a cike kowane kwari,Za a baje kowane dutse.Tuddai za su zama fili,Ƙasa mai kururrumai za ta zama sumul.

Karanta cikakken babi Ish 40