Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 38:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A lokacin nan sai sarki Hezekiya ya kamu da rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Sai annabi Ishaya, ɗan Amoz, ya je wurinsa domin ya gaishe shi, ya ce masa, “Ubangiji ya ce ka kintsa kome daidai, gama ba za ka warke ba. Ka yi shirin mutuwa.”

2. Hezekiya kuwa ya juya wajen bango ya yi addu'a, ya ce,

3. “Ya Ubangiji, ka tuna, na bauta maka da aminci da biyayya, na kuma yi ƙoƙarin aikata abin da kake so in yi.” Sai ya fara kuka mai zafi.

4. Sa'an nan Ubangiji ya umarci Ishaya,

5. cewa ya koma wurin Hezekiya ya faɗa masa, “Ni, Ubangiji Allah na kakanka Dawuda, na ji addu'arka, na kuma ga hawayenka, zan bar ka ka ƙara shekara goma sha biyar nan gaba.

6. Zan cece ka, da wannan birni na Urushalima, daga Sarkin Assuriya, zan ci gaba da kiyaye birnin.”

7. Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ubangiji zai nuna maka alama da za ta tabbatar maka zai cika alkawarinsa.

8. Ubangiji zai komar da inuwa baya da taki goma, bisa ga ma'aunin rana na sarki Ahaz.” Inuwa kuwa ta koma da baya daga fuskar rana har mataki goma.

9. Bayan da Hezekiya ya warke daga rashin lafiyarsa, sai ya rubuta wannan waƙar yabo.

10. Na zaci a gaɓar ƙarfinaZan tafi lahira,Ba zan ƙara rayuwa ba.

Karanta cikakken babi Ish 38