Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 34:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku zo, ku jama'ar dukan al'ummai! Ku tattaru ku kasa kunne. Bari dukan duniya, da kowane mai zama cikinta, ya zo nan ya kasa kunne.

2. Ubangiji yana fushi da al'ummai duka, da kuma dukan sojojinsu. Ya zartar musu da hukuncin hallaka.

3. Ba za a binne gawawwakinsu ba, amma za a bar su can, su ruɓe, su yi ɗoyi, duwatsu kuma za su yi ja wur da jini.

4. Za a murtsuke rana, da wata, da taurari su zama ƙura. Sararin sama zai shuɗe kamar yadda ake naɗe littafi, taurari kuma su faɗo kamar yadda ganyaye suke karkaɗewa daga itacen inabi ko na ɓaure.

5. Ubangiji ya shirya takobinsa a can Sama, yanzu kuwa zai buga Edom, wato mutanen can da ya zartar musu da hukuncin hallaka.

Karanta cikakken babi Ish 34