Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 32:15-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Amma Allah zai ƙara aiko mana da Ruhunsa. Ƙasar da ta zama marar amfani za ta komo mai dausayi, gonaki kuma za su ba da amfani mai yawa.

16. A ko'ina a ƙasar za a aikata adalci da gaskiya.

17. Gama kowa zai yi abin da yake daidai, za a sami salama da zaman lafiya har abada.

18. Gidajen jama'ar Allah za su zama da salama da zaman lafiya, ba abin da zai dame su.

19. (Amma ƙanƙara za ta faɗo a jeji, za a kuma rurrushe birni.)

20. Kowa zai yi murna da ruwan sama mai yawa domin amfanin gona, da kuma lafiyayyiyar makiyaya domin jakuna da shanu.

Karanta cikakken babi Ish 32