Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 32:10-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Zai yiwu ku wadatu yanzu, amma baɗi war haka za ku fid da zuciya, gama ba inabin da za ku tattara.

11. Kuna ta zaman jin daɗi, ba abin da yake damunku, amma yanzu ku yi rawar jiki don tsoro! Ku tuɓe tufafinku ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku.

12. Ku bugi ƙirjinku don baƙin ciki, gama an lalatar da gonaki masu dausayi da kuma gonakin inabi,

13. ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya ne suke girma a ƙasar jama'ata. Ku yi kuka domin dukan gidajen da mutane suke murna a cikinsu dā, domin kuma birnin da yake cike da jin daɗi a dā.

14. Har ma za a bar fādar, babban birnin sarauta kuma za a gudu a bar shi gaba ɗaya. Gidaje kuma da kagaran da take tsaronsu za su zama rusassu har abada. A can jakunan jeji za su yi ta zarya, tumaki kuma za su sami wurin kiwo.

15. Amma Allah zai ƙara aiko mana da Ruhunsa. Ƙasar da ta zama marar amfani za ta komo mai dausayi, gonaki kuma za su ba da amfani mai yawa.

16. A ko'ina a ƙasar za a aikata adalci da gaskiya.

17. Gama kowa zai yi abin da yake daidai, za a sami salama da zaman lafiya har abada.

18. Gidajen jama'ar Allah za su zama da salama da zaman lafiya, ba abin da zai dame su.

Karanta cikakken babi Ish 32