Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 30:5-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. duk da haka jama'ar Yahuza za su yi da na sani, da suka dogara ga al'ummar da ba abar dogara ba ce, al'ummar da ba ta daɗa musu kome a lokacin da suke sa zuciya ga taimako ba.”

6. Wannan shi ne jawabin da Allah ya yi a kan dabbobin da suke kudancin hamada, “Jakadu sun yi tafiya a ƙasa mai hatsari, inda zakoki suke, inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke. Suna labta wa jakunansu da raƙumansu kayayyaki masu tsada da za su kai gaisuwa ga al'ummar da ba za ta taimake su da kome ba.

7. Taimakon da Masar za ta yi marar amfani ne. Don haka na yi mata laƙabi, ‘Macijin da ba ya yin kome.’ ”

8. Allah ya faɗa mini in rubuta a littafi yadda mutane suke, saboda ya zama tabbatacciyar shaida a kansu.

9. A kullum suna tayar wa Allah, a kullum ƙarya suke yi, a kullum suna ƙin kasa kunne ga koyarwar Allah.

10. Sukan faɗa wa annabawa su yi shiru. Sukan ce, “Kada ku yi mana magana a kan abin da yake daidai. Ku faɗa mana abin da muke so mu ji ne kawai. Bari mu ci gaba da ruɗewarmu.

11. Tashi daga nan, kada ku toshe mana hanya. Ba ma so mu ji kome game da Allah Mai Tsarki na Isra'ila.”

12. Amma wannan shi ne abin da Allah Mai Tsarki na Isra'ila ya ce, “Kun yi banza da abin da nake faɗa muku, kuna dogara ga aikin kamakarya da yin zamba.

13. Kun yi laifi. Kuna kamar bango wanda ya tsage daga bisa har ƙasa. Za ku fāɗi ba zato ba tsammani.

14. Za a ragargaza ku kamar tukunyar yumɓu, da mummunar ragargazawa har da ba za a sami 'yar katangar da za a ɗauki garwashin wuta ba, ko a ɗebo ruwa daga randa.”

15. Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya ce wa jama'a, “Ku komo gare ni a natse, ku dogara gare ni. Sa'an nan za ku zama ƙarfafa ku zauna lafiya.” Amma ba ku yarda ba!

16. A maimakon haka sai kuka shirya ku tsere wa maƙiyanku a kan dawakai masu gudu. Daidai ne, tilas ku tsere! Tsammani kuke saurin gudun dawakanku ya isa, amma waɗanda za su fafare ku sun fi ku gudu!

17. Dubunku za su gudu da ganin abokin gābanku ɗaya, abokan gāba biyar sun isa su sa dukanku ku gudu. Ba abin da zai ragu daga cikin rundunar sojojinku, sai sandan tutarku kaɗai da take kan tudu.

Karanta cikakken babi Ish 30