Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 28:23-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Ku kasa kunne ga abin da nake cewa, ku mai da hankali ga abin da nake faɗa muku.

24. Manomi ba zai dinga huɗar gonakinsa har abada ba, ya yi ta shirya su domin shuka.

25. Da zarar ya shirya ƙasar yakan shusshuka ganyayen ci, kamar su kanumfari da ɗaɗɗoya, yakan kuma dasa kunyoyin alkama da na sha'ir, a gyaffan gonakin kuwa yakan shuka hatsi.

26. Ya san yadda zai yi aikinsa, gama Allah ya koya masa.

27. Ba ya bugun kanumfari da ɗaɗɗoya da ƙaton kulki, a maimakon haka yakan yi da 'yan sanduna sirara.

28. Ba zai yi ta bugun alkama, har ya ɓata tsabar ba, ya san yadda zai sussuke alkamarsa, ba tare da ya ɓata tsabarta ba.

29. Dukan wannan hikima daga wurin Ubangiji Mai Runduna ne. Shirye-shiryen da Allah ya yi na hikima ne kullum kuwa sukan yi nasara!

Karanta cikakken babi Ish 28