Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 28:10-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Yana ƙoƙari ya koya mana baƙaƙe baƙaƙe, da shaɗara shaɗara, da babi babi.”

11. Idan ba za ku saurare ni ba, to, Allah zai yi amfani da baƙi masu magana da harshen da ba ku sani ba, su koya muku darasi.

12. Ya miƙa muku hutawa da wartsakewa, amma kun ƙi saurarawa gare shi.

13. Saboda haka ne Ubangiji zai koya muku baƙaƙe baƙaƙe, da shaɗara shaɗara, da babi babi. Sa'an nan kowane ɗaga ƙafar da kuka yi, za ku yi tuntuɓe, za a yi muku rauni, a kama ku a tarko, a kai ku kurkuku.

Karanta cikakken babi Ish 28