Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 25:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Ubangiji, kai ne Allahna, Zan ɗaukaka ka, in yabi sunanka.Ka aikata al'amura masu banmamaki,Ka tafiyar da su da aminci,Wato bisa ga shirin da ka yi tuntuni.

2. Ka mai da birane kufaiKa lalatar da kagaransu,Wuraren da maƙiya suka gina kuwa,An shafe su har abada.

3. Jama'ar al'ummai masu iko za su yabe ka,Za a ji tsoronka a biranen mugayen al'ummai.

4. Matalauta da 'yan ƙaƙa naka yi sun sheƙa zuwa wurinka,Sun sami zaman lafiya a lokatan wahala.Ka ba su mafaka daga hadura,Ka inuwantar da su daga matsanancin zafi.Mugaye sukan tasar musu kamar hadirin ƙanƙara,

5. Kamar fari a ƙeƙasasshiyar ƙasa.Amma kai, ya Ubangiji, ka rufe bakin abokan gābanmu,Ka sa hayaniyar mugaye ta yi tsit,Kamar yadda girgije yake sanyaya zafin rana.

6. A kan Dutsen Sihiyona Ubangiji Mai Runduna zai shirya wa dukan sauran al'umman duniya biki da abinci irin na adaras da ruwan inabi mafi kyau.

Karanta cikakken babi Ish 25