Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 24:13-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Wannan shi ne abin da zai sami kowace al'umma ko'ina a duniya. Zai zama kamar ƙarshen kaka sa'ad da aka karkaɗe zaitun daga kowane itace, aka kuma gama tsinke 'ya'yan inabi daga kurangar inabi.

14. Waɗanda suka tsira za su raira waƙa don farin ciki. Waɗanda suke wajen yamma za su ba da labarin girman Allah,

15. waɗanda suke wajen gabas kuma za su yabe shi. Jama'ar da take zaune a gefen teku za su yabi Ubangiji, Allah na Isra'ila.

16. Daga manisantan wurare na duniya za mu ji waƙoƙin yabon Isra'ila, al'umma adala.Amma ba ni da sauran sa zuciya! Lalacewa nake yi! Maciya amana suna ta cin amana, cin amanarsu sai gaba gaba yake yi.

17. Ya jama'ar duniya, razana, da wushefe, da tarkuna suna jiranku.

18. Duk wanda ya yi ƙoƙarin tserewa daga razana zai fāɗa cikin wushefe, wanda kuma ya tsere daga wushefe za a kama shi a tarko. Za a kwararo ruwa daga sama kamar da bakin ƙwarya, harsashin ginin duniya zai jijjigu.

Karanta cikakken babi Ish 24