Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 23:13-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. (Mutanen Babila ne, ba na Assuriya ba, waɗanda suka bar namomin jeji su murƙushe Taya. Mutanen Babila ne suka gina hasumiya, suka ragargaza kagarar Taya suka bar birnin kango.)

14. Ku yi hargowar baƙin ciki ku matuƙan jiragen teku! An hallaka birnin da kuke dogara gare shi.

15. Lokaci yana zuwa da za a manta da Taya har shekara saba'in, gwargwadon kwanakin sarki. Bayan waɗannan shekaru kuma, Taya za ta yi waƙa irin ta karuwa, cewa

16. “Ɗauki garayarki, kewaya cikin gari,Ayya, an manta da karuwa!Yi kiɗa, sāke raira waƙoƙinki,Don ki komo da masoyanki.”

17. Bayan shekara saba'in ɗin, Ubangiji zai bar Taya ta koma a kan cinikinta na dā, za ta ba da kanta ijara ga dukan mulkokin duniya.

18. Kuɗin da ta samu ta kasuwanci za a keɓe wa Ubangiji. Ba za ta tara wa kanta ba, amma waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada su za su yi amfani da kuɗinta don su saya wa kansu abinci da sutura da suke bukata.

Karanta cikakken babi Ish 23