Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 23:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wannan shi ne jawabi a kan Taya.Ku yi hargowa ta baƙin ciki, ku matuƙan jiragen ruwan teku! An lalatar da tashar jiragen ruwan garinku na Taya. Gidajenta da gaɓarta sun rurrushe. Sa'ad da jiragen ruwanku suka komo daga Kubrus za ku ji labarin.

2. Ku yi kuka ku fataken Sidon! Kun aika da mutane

3. a hayin teku don su yi muku saye da sayarwa na hatsin da ake nomawa a Masar, su yi hulɗa da dukan sauran al'umma.

4. Birnin Sidon, ke abar kunya ce! Teku da manyan zurfafan ruwaye sun yanke hulɗa da ke, sun ce, “Ban taɓa haihuwar 'ya'ya ba, ban taɓa goyon 'ya'ya mata ko maza ba.”

5. Har Masarawa ma za su firgita su razana, sa'ad da suka ji, cewa an hallakar da Taya.

6. Ku yi ruri da baƙin ciki, ku jama'ar bakin teku, ku yi ƙoƙari ku tsere zuwa Tarshish!

7. Ya yiwu kuwa a ce wannan Taya ce birnin farin ciki, wadda aka kafa ta tuntuni? Wannan kuwa ita ce birnin da yake aikawa da mutane hayin teku su kafa nahiyoyi?

8. Wane ne wannan wanda ya shirya ya aukar wa Taya da wannan duka, wannan muhimmiyar alkarya, wadda fatakenta hakimai ne, waɗanda ake ɗaukaka su fiye da sauran mutane a duniya?

9. Ubangiji Mai Runduna ne ya shirya wannan! Ya shirya haka ne don ya kawo ƙarshen girmankanta saboda abin da suka aikata, don ya ƙasƙantar da manyan mutanenta.

10. Ku je ku nomi ƙasarku jama'ar nahiyoyin Tarshish! Ba wanda zai ƙara kiyaye ku.

11. Ubangiji ya miƙa dantsensa a kan tekun, ya hamɓarar da mulkoki. Ya umarta a lalatar da manyan biranen ciniki na Taya.

12. Birnin Sidon, farin cikinki ya ƙare. Ana zaluntar jama'arki, ko da za su tsere zuwa Kubrus duk da haka ba za su zauna lafiya ba.

13. (Mutanen Babila ne, ba na Assuriya ba, waɗanda suka bar namomin jeji su murƙushe Taya. Mutanen Babila ne suka gina hasumiya, suka ragargaza kagarar Taya suka bar birnin kango.)

14. Ku yi hargowar baƙin ciki ku matuƙan jiragen teku! An hallaka birnin da kuke dogara gare shi.

Karanta cikakken babi Ish 23