Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 2:6-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ya Allah, ka rabu da jama'arka, zuriyar Yakubu. Ƙasa ta cika da ayyukan sihiri da aka kawo daga Gabas, daga kuma ƙasar Filistiya. Jama'a suna bin baƙin al'adu.

7. Ƙasarsu tana cike da azurfa da zinariya, dukiyarsu kuma ba iyaka. Ƙasarsu tana cike da dawakai, karusansu kuma ba iyaka.

8. Ƙasarsu tana cike da gumaka, suna sujada ga abubuwan da suka yi da hannuwansu.

9. Za a ƙasƙantar da kowane mutum, a kunyata shi. Kada ka gafarta musu, ya Ubangiji!

10. Za su ɓuya a cikin kogwannin duwatsu, ko su haƙa ramummuka a ƙasa, suna ƙoƙarin tserewa daga fushin Ubangiji, ko su ɓuya daga ikonsa da ɗaukakarsa!

11. Rana tana zuwa sa'ad da girmankan 'yan adam zai ƙare, zai kuma lalatar da fāriyar 'yan adam. Sa'an nan Ubangiji ne kaɗai za a ɗaukaka.

12. A wannan rana, Ubangiji Mai Runduna zai ƙasƙantar da kowane mai iko, da kowane mai girmankai, da kowane mai fāriya.

13. Zai hallaka dogayen itatuwan al'ul na Lebanon, da dukan itatuwan oak na ƙasar Bashan.

14. Zai baje duwatsu da tuddai masu tsayi,

15. da kowace doguwar hasumiya, da ganuwar kowace kagara.

16. Zai nutsar da jiragen ruwa mafi girma mafi kyau.

17. Girmankan ɗan adam zai ƙare, za a hallakar da fāriyar ɗan adam, Ubangiji ne kaɗai za a ɗaukaka sa'ad da wannan rana ta yi,

18. za a shafe gumaka ƙaƙaf.

19. Mutane za su ɓuya a kogwannin duwatsu, ko su haƙa ramummuka a ƙasa, suna ƙoƙarin tserewa daga fushin Ubangiji, ko su ɓuya daga ikonsa da ɗaukakarsa, sa'ad da ya zo domin ya girgiza duniya.

20. Sa'ad da wannan rana ta yi za su zubar da gumakan da suka yi na zinariya da azurfa, za su bar wa ɓeraye da jemagu.

21. Sa'ad da Ubangiji ya zo domin ya girgiza duniya, jama'a za su ɓuya a cikin kogwannin tuddai da ramummukan duwatsu, suna ƙoƙari su ɓuya daga fushinsa, ko su ɓuya daga ikonsa da ɗaukakarsa.

Karanta cikakken babi Ish 2