Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 2:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ga jawabin da Allah ya faɗa wa Ishaya ɗan Amoz a kan Yahuza da Urushalima.

2. A kwanaki masu zuwa,Dutse inda aka gina Haikali zai zama mafi tsayi duka.Al'ummai da yawa za su zo su yi ta bumbuntowa su zo gare shi.

3. Jama'arsu za su ce,“Bari mu haura zuwa tudun Ubangiji,Zuwa ga Haikalin Allah na Isra'ila.Za mu koyi abin da yake so mu yi,Za mu yi tafiya a hanyar da ya zaɓa.Koyarwar Ubangiji daga Urushalima take zuwa,Daga Sihiyona yake magana da jama'arsa.”

4. Zai sulhunta jayayyar da yake tsakanin manyan al'ummai,Za su mai da takubansu garemani,Masunsu kuma su maishe su wuƙaƙen aske itace,Al'ummai ba za su ƙara fita zuwa yaƙi ba,Ba za su ƙara koyon yaƙi ba.

5. Yanzu fa, zuriyar Yakubu, bari mu yi tafiya a cikin hasken da Ubangiji ya ba mu!

6. Ya Allah, ka rabu da jama'arka, zuriyar Yakubu. Ƙasa ta cika da ayyukan sihiri da aka kawo daga Gabas, daga kuma ƙasar Filistiya. Jama'a suna bin baƙin al'adu.

7. Ƙasarsu tana cike da azurfa da zinariya, dukiyarsu kuma ba iyaka. Ƙasarsu tana cike da dawakai, karusansu kuma ba iyaka.

8. Ƙasarsu tana cike da gumaka, suna sujada ga abubuwan da suka yi da hannuwansu.

Karanta cikakken babi Ish 2