Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 19:15-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. A Masar duka, attajiri da matalauci, ƙarami ko babba, ba wanda zai iya yin wani taimako.

16. Lokaci zai yi in da zuciyar mutanen Masar za ta narke kamar mata. Za su yi rawar jiki da razana lokacin da suka ga Ubangiji Mai Runduna ya miƙa hannunsa don ya hukunta su.

17. Mutanen Masar za su firgita saboda Yahuza, kowane lokaci za su tuna da ƙaddarar da Ubangiji Mai Runduna ya shirya dominsu.

18. A wannan rana, za a yi amfani da harshen Ibrananci a birane biyar na Masar. Mutanen da suke can za su riƙa yin rantsuwarsu da sunan Ubangiji Mai Runduna. Za a sa wa ɗaya daga cikin biranen nan suna, “Birnin Hallaka.”

19. A wannan rana, za a gina wa Ubangiji bagade a ƙasar Masar, za a keɓe masa ginshiƙi na dutse a kan iyakar Masar.

20. Za su zama alamu na kasancewar Ubangiji Mai Runduna a Masar. Sa'ad da aka zalunci mutanen da suke can, za su yi kira ga Ubangiji su nemi taimako, zai aika musu wanda zai kuɓutar da su.

21. Ubangiji zai bayyana kansa ga mutanen Masar, sa'ad da ya yi haka kuwa, za su karɓe shi, su yi masa sujada, su kuma kawo masa hadayu da sadakoki. Za su yi masa alkawarai ƙwarara, su kuwa cika abin da suka alkawarta.

22. Ubangiji zai hukunta Masarawa, amma zai warkar da su. Za su juyo gare shi, shi kuma zai ji addu'o'insu ya warkar da su.

23. A wannan rana, za a yi wata babbar hanya tsakanin Masar da Assuriya. Mutanen ƙasashen nan biyu za su yi ta kai da kawowa tsakaninsu, al'ummai biyu za su yi sujada tare.

24. A wannan rana, za a lasafta Isra'ila tare da Masar da Assuriya, waɗannan al'ummai uku za su zama albarka ga dukan duniya.

Karanta cikakken babi Ish 19