Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 11:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Gidan sarautar Dawuda kamar itacen da aka sare ne, amma kamar yadda rassa sukan toho daga cikin kututture, haka nan za a sami sabon sarki daga zuriyar Dawuda.

2. Ikon Ubangiji zai ba shi hikima,Da sani, da gwaninta yadda zai mallaki mutanensa.Zai kuwa san nufin Ubangiji, ya kuma yi tsoronsa,

3. Zai ji daɗin yin hidimarsa.Ba zai yi shari'ar ganin ido ko ta waiwai ba.

4. Zai yi wa matalauta shari'a daidai.Zai kuma kāre hakkin masu tawali'u.Bisa ga umarninsa za a hukunta ƙasar,Mugaye za su mutu.

5. Zai yi mulkin mutanensa da adalci da mutunci.

6. Kyarketai da tumaki za su zauna tare lafiya.Damisoshi za su kwanta tare da 'yan awaki.'Yan maruƙa da kwiyakwiyan zaki za su yi kiwo tare,Ƙananan yara ne za su lura da su.

7. Shanu da beyar za su yi kiwo tare,'Yan maruƙansu da kwiyakwiyansu za su kwanta lafiya.Zaki zai ci ciyawa kamar sā.

8. Jariri zai yi wasa kusa da maciji mai mugun dafiAmma ba zai cuta ba.

9. A kan Sihiyona, dutse tsattsarka,Ba wani macuci ko mugu.Ƙasar za ta cika da sanin UbangijiKamar yadda tekuna suke cike da ruwa.

Karanta cikakken babi Ish 11