Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 1:25-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Zan hukunta ku. Zan tace ku kamar yadda ake tace ƙarfe, in kawar da dukan ƙazantarku.

26. Zan ba ku shugabanni da mashawarta kamar waɗanda kuke da su dā can. Sa'an nan za a ce da Urushalima adala, amintaccen birni.”

27. Gama Ubangiji mai adalci ne, zai ceci Urushalima da dukan wanda ya tuba a can.

28. Amma zai ragargaza dukan wanda ya yi zunubi, ya tayar gāba da shi, zai kashe duk wanda ya rabu da shi.

29. Za ku yi da na sani, ku da kuka taɓa yin sujada ga itatuwa da dashe-dashen masujada.

30. Za ku bushe kamar busasshen itacen oak, kamar lambun da ba wanda yake ba shi ruwa.

31. Daidai kamar yadda busasshen itacen da tartsatsin wuta ya fāɗa wa, haka mutane masu iko za su hallaka ta wurin mugayen ayyukansu, ba wanda zai iya hana a hallaka su.

Karanta cikakken babi Ish 1