Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 8:8-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ƙaƙa za ku ce, “Muna da hikima,Dokar Ubangiji tana tare da mu”?Ga shi kuwa, alkalamin ƙarya namagatakarda, ya yi ƙarya.

9. Za a kunyatar da masu hikima.Za su tsorata, za a kuma tafi da su.Ga shi, sun ƙi maganar Ubangiji.Wace hikima suke da ita?

10. Saboda haka zan ba da matansu gawaɗansu,Gonakinsu kuma ga waɗanda sukecinsu da yaƙi,Saboda tun daga ƙarami har zuwababbaKowannensu yana haɗamar cinmuguwar riba,Tun daga annabawa zuwa firistociKowannensu aikata ha'inci yake yi.

11. Sun warkar da raunin mutanenasama sama,Suna cewa, “Lafiya, lafiya,” alhalikuwa ba lafiya.

Karanta cikakken babi Irm 8