Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 8:17-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. “Ni Ubangiji na ce, ‘Zan aiko mukuda macizai, da kāsā,Waɗanda ba su da makari,Za su sassare ku.’ ”

18. Baƙin cikina ya fi ƙarfin warkewa,Zuciyata ta ɓaci ƙwarai!

19. Ku ji kukan jama'ata ko'ina aƙasar,“Ubangiji, ba shi a Sihiyonane?Sarkinta ba ya a cikinta ne?”Ubangiji ya ce,“Me ya sa suka tsokane ni dasassaƙaƙƙun gumakansu,Da baƙin gumakansu?”

20. Mutane suna ta cewa,“Damuna ta ƙare, kaka kuma tawuce,Amma ba a cece mu ba.”

21. Raunin da aka yi wa jama'ata,Ya yi wa zuciyata rauni.Ina makoki, tsoro kuma ya kama niƙwarai.

22. Ba abin sanyayawa a Gileyad ne?Ba mai magani a can ne?Me ya sa ba a warkar da jama'ataba?

Karanta cikakken babi Irm 8