Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 8:10-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Saboda haka zan ba da matansu gawaɗansu,Gonakinsu kuma ga waɗanda sukecinsu da yaƙi,Saboda tun daga ƙarami har zuwababbaKowannensu yana haɗamar cinmuguwar riba,Tun daga annabawa zuwa firistociKowannensu aikata ha'inci yake yi.

11. Sun warkar da raunin mutanenasama sama,Suna cewa, “Lafiya, lafiya,” alhalikuwa ba lafiya.

12. Ko sun ji kunyaSa'ad da suka aikata ayyuka masubanƙyama?A'a, ba su ji kunya ba ko kaɗan,Fuskarsu ko gezau ba ta yi ba.Domin haka za su faɗi tare dafāɗaɗɗu,Sa'ad da na hukunta su, za a ci su dayaƙi.Ni Ubangiji na faɗa.’

13. “Ni Ubangiji na ce,‘Sa'ad da zan tattara su kamaramfanin gona,Sai na tarar ba 'ya'ya a kurangarinabi,Ba 'ya'ya kuma a itacen ɓaure,Har ganyayen ma sun bushe.Abin da na ba su kuma ya kuɓucemusu.Ni Ubangiji na faɗa.’ ”

14. Mutanen Urushalima sun ce,“Don me muke zaune kawai?Bari mu tattaru, mu tafi cikingaruruwa masu garu,Mu mutu a can,Gama Ubangiji Allahnmu yaƙaddara mana mutuwa,Ya ba mu ruwan dafi,Domin mun yi masa laifi.

15. Mun sa zuciya ga salama, amma balafiya,Mun sa zuciya ga lokacin samunwarkewa,Amma sai ga razana!

16. Daga Dan, an ji firjin dawakai.Dakan ƙasar ta girgiza sabodahaniniyar ingarmunsu.Sun zo su cinye ƙasar duk da abinda suke cikinta,Wato da birnin da mazaunacikinsa.”

Karanta cikakken babi Irm 8