Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 6:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Ya ku mutanen Biliyaminu, kugudu neman mafaka,Daga cikin Urushalima!Ku busa ƙaho a Tekowa,Ku ba da alama a Bet-akkerem,Gama masifa da babbar halaka sunfito daga arewa.

2. Ya Sihiyona, ke kyakkyawarmakiyaya ce, zan hallaka abin dakika hahhaifa.

3. Makiyaya da garkunansu za su zowurinki,Za su kafa alfarwansu kewaye da ke,Kowa zai yi kiwo a makiyayarki.

4. Za su ce, ‘Mu yi shiri mu fāɗa matada yaƙi!Ku tashi, mu fāɗa musu da tsakarrana!’Sai kuma suka ce, ‘Kaitonmu, garana tana faɗuwa, ta yi ruɗa-kuyangi.

5. Mu tashi mu fāɗa mata da dare,Mu lalatar da fādodinta.’ ”

6. Ubangiji Mai Runduna ya ce,“Ku sassare itatuwanta,Ku tula ƙasa kewaye daUrushalima,Dole in hukunta wannan birnisaboda ba kome cikinsa saizalunci,

7. Kamar yadda rijiya take da ruwagarau,Haka Urushalima take damuguntarta,Ana jin labarin kama-karya da nahallakarwa a cikinta,Kullum akwai cuce-cuce, da raunukaa gabana,

Karanta cikakken babi Irm 6