Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 51:47-51 Littafi Mai Tsarki (HAU)

47. Saboda haka kwanaki suna zuwa,Sa'ad da zan hukunta gumakanBabila,Za a kunyatar da dukan ƙasarBabila,Dukan matattunta za su faɗi atsakiyarta.

48. Sa'an nan sama da duniya, da dukanabin da take cikinsu,Za su raira waƙar farin ciki,Domin masu hallakarwa daga arewada za su auko mata,Ni Ubangiji na faɗa.”

49. Babila za ta fāɗi,Saboda mutanen Isra'ila da dukanmutanen duniya waɗanda takashe.

50. Ku waɗanda kuka tsere wa takobi!Ku gudu! Kada ku tsaya!Ku tuna da Ubangiji a can nesa indakuke,Ku kuma yi ta tunawa daUrushalima.

51. Mun sha kunya saboda zargin da akeyi mana,Kunya ta rufe mu,Gama baƙi sun shiga tsarkakanwurare na Haikalin Ubangiji.

Karanta cikakken babi Irm 51