Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 49:6-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. “Amma daga baya zan saAmmonawa su wadata kuma,Ni Ubangiji na faɗa.”

7. Ga abin da Ubangiji Mai Rundunaya faɗa a kan Edom,“Ba hikima kuma a cikin Teman?Shawara ta lalace a wurin masubasira?Hikima ta lalace ne?

8. Ku mazaunan Dedan, ku juya, kugudu,Ku ɓuya cikin zurfafa,Gama zan kawo masifa a kan IsuwaA lokacin da zan hukunta shi,

9. Idan masu tsinkar 'ya'yan inabi sunzo wurinkaBa za su rage abin kala ba?Idan kuma ɓarayi sun zo da dare,Za su ɗauki iyakacin abin da suke sokurum.

10. Amma na tsiraita Isuwa sarai,Na buɗe wuraren ɓuyarsa,Har bai iya ɓoye kansa ba,An hallakar da mutanen IsuwaTare da 'yan'uwansa damaƙwabtansa,Ba wanda ya ragu.

11. Ka bar marayunka, ni zan rayar dasu.Matanka da mazansu sun mutu,Sai su dogara gare ni.”

12. Ubangiji ya ce, “Ga shi, waɗanda ba a shara'anta su ga shan ƙoƙon hukunci ba, za su sha shi, to, kai za ka kuɓuta? Ba za ka kuɓuta ba, amma lalle za ka sha shi!

13. Gama ni Ubangiji na rantse da zatina, cewa Bozara za ta zama abar tsoro, da abar dariya, da kufai, da abar la'ana. Dukan garuruwanta za su zama kufai har abada.”

14. Irmiya ya ce,“Na karɓi saƙo daga wurinUbangiji.An aiki jakada a cikin al'ummaicewa,‘Ku tattara kanku, ku zo ku yi gābada ita,Ku tasar mata da yaƙi!’

Karanta cikakken babi Irm 49