Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 49:33-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

33. Hazor za ta zama kufai har abada,wurin zaman diloli,Ba wanda zai zauna a ciki, ba wandakuma zai yi zaman baƙunci a wurin.”

34. Maganar da Ubangiji ya yi wa annabi Irmiya a kan Elam a farkon sarautar Zadakiya Sarkin Yahuza.

35. Ubangiji Mai Runduna ya ce,“Zan karya bakan Elam, indaƙarfinta yake.

36. Zan sa iska ta hura a kan Elam dagakusurwoyi huɗu na samaniya.Za ta watsar da mutane ko'ina,Har ba ƙasar da za a rasa mutuminElam a ciki.

37. Zan sa mutanen Elam su ji tsoronmaƙiyansu waɗanda suke nemanransu.Da zafin fushina zan kawo musumasifa,In sa a runtume su da takobi,Har in ƙare su duka,Ni Ubangiji na faɗa.

38. Zan kafa gadon sarautata a Elam,Zan hallaka sarkinta dashugabanninta.

39. Amma daga baya zan sa Elam kumata wadata.Ni Ubangiji na faɗa.”

Karanta cikakken babi Irm 49