Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 44:17-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Za mu aikata dukan abin da muka faɗa. Za mu miƙa wa gunkiyan nan, wato sarauniyar sama, hadayu, da hadayu na sha kamar yadda kakanninmu, da shugabanninmu suka yi a garuruwan Yahuza, da kan titunan Urushalima. A lokacin kuwa muna da abinci a wadace, muka arzuta, ba wata wahala.

18. Amma tun da muka daina miƙa wa sarauniyar sama hadayu, da hadayu na sha, ba mu da kome, sai dai takobi da yunwa suke kashe mu.”

19. Mata kuma suka ce, “Sa'ad da muka toya waina ga siffar sarauniyar sama, muka miƙa mata hadayu, da hadayu na sha, ai, mazanmu sun goyi bayan abin da muka yi.”

20. Sa'an nan Irmiya ya ce wa dukan mutane, mata da maza, waɗanda suka ba shi irin amsan nan, ya ce,

21. “A kan turaren da ku da kakanninku, da sarakunanku, da shugabanninku, da mutanen ƙasar, kuka ƙona a garuruwan Yahuza da a titunan Urushalima, kuna tsammani Ubangiji bai san su ba, ko kuna tsammani ya manta?

22. Ubangiji ba zai yarda da mugayen ayyukanku ba, da ƙazantarku da kuka aikata, don haka ƙasarku a yau ta zama kufai ba mai zama a cikinta. Ta zama abin ƙyama da la'ana.

23. Saboda kun ƙona turare, kun yi wa Ubangiji zunubi, ba ku yi biyayya da muryarsa ba, ba ku kiyaye dokokinsa, da umarnansa, da sharuɗansa ba, shi ya sa wannan masifa ta auko muku a yau.”

24. Sai Irmiya ya ce wa dukan mutane duk da mata, “Ku ji maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuza da suke a Masar.

25. Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, ‘Ku da matanku kun faɗa da bakinku, kun kuma aikata da hannuwanku, cewa za ku aikata wa'adodin da kuka yi na ƙona turare, da miƙa hadayu na sha ga sarauniyar sama.’ To, sai ku tabbatar da wa'adodinku, ku cika su!

26. Domin haka ku ji maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuza da yake zaune a ƙasar Masar. ‘Ni Ubangiji na rantse da sunana Maɗaukaki, cewa ba zan yarda kuma wani mutumin Yahuza da yake ƙasar Masar ya ambaci sunana da yin rantsuwa, cewa ya rantse da zatin Ubangiji ba.’

27. Ga shi, ina lura da su, ba domin alheri ba, amma domin in aukar musu da masifa. Takobi da yunwa za su hallaka dukan mutanen Yahuza waɗanda suke a ƙasar Masar.

28. ‘Yan kaɗan ne za su tsere wa takobi, za su kuwa koma daga ƙasar Masar zuwa ƙasar Yahuza. Sauran mutanen Yahuza da suka ragu, waɗanda suka zo Masar da zama, za su sani ko maganar wa za ta cika, tasu ko kuwa tawa.

29. Ni Ubangiji na ce, wannan zai zama muku alama, cewa zan hukunta ku a wannan wuri domin ku sani lalle maganata ta aukar muku da masifa za ta cika.

30. Zan kuma ba da Fir'auna Hofra, Sarkin Masar, a hannun abokan gabansa, da waɗanda suke neman ransa, kamar yadda na ba da Zadakiya, Sarkin Yahuza, a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila wanda ya zama abokin gābansa, ya kuwa nemi ransa.’ ”

Karanta cikakken babi Irm 44