Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 43:10-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. ka kuma ce musu, ‘In ji Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ga shi, zan aika wa bawana Nebukadnezzar ya zo ya kafa kursiyin sarautarsa a kan duwatsun nan waɗanda na ɓoye. Zai buɗe babbar alfarwarsa a wurin.

11. Nebukadnezzar zai zo ya buga ƙasar Masar. Zai ba annoba waɗanda aka ƙaddara su ga annoba, waɗanda aka ƙaddara ga bauta, za a kai su bauta. Waɗanda aka ƙaddara ga takobi, za su mutu ta takobi.

12. Zai cinna wa gidajen gumakan Masar wuta, zai ƙone su, ya tafi da waɗansu, zai tsabtace ƙasar Masar kamar yadda makiyayi yakan kakkaɓe ƙwarƙwata daga cikin tufafinsa, zai kuwa tashi daga wurin lafiya.

13. Zai kuma farfashe al'amudan duwatsu na On a ƙasar Masar. Zai ƙone gidajen gumakan Masar da wuta.’ ”

Karanta cikakken babi Irm 43