Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 38:20-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Irmiya kuwa ya ce masa, “Ba za a bashe ka gare su ba. Kai dai ka yi biyayya da maganar Ubangiji wadda nake faɗa maka yanzu. Yin haka zai fi maka amfani, za ka tsira.

21. Amma idan ka ƙi miƙa wuya, to, ga abin da Ubangiji ya nuna mini a wahayi.

22. Ga shi, dukan matan da suka ragu a gidan Sarkin Yahuza, za a kai su wurin sarakunan Sarkin Babila, suna cewa,‘Aminanka sun ruɗe ka,Sun rinjaye ka.Yanzu sun ga ƙafafunka sun nutsecikin laka,Sai suka rabu da kai.’

23. “Dukan matanka da 'ya'yanka za a kai su wurin Kaldiyawa, kai kanka kuma ba za ka tsere musu ba, amma Sarkin Babila zai kama ka, birnin kuma za a ƙone shi da wuta.”

24. Sai Zadakiya ya ce wa Irmiya, “Kada ka bar wani ya san wannan magana, kai kuwa ba za a kashe ka ba.

25. Idan sarakuna suka ji, wai na yi magana da kai, in suka zo wurinka, suka ce, ‘Ka faɗa mana abin da ka faɗa wa sarki da abin da sarki ya faɗa maka, kada ka ɓoye mana kome mu kuwa ba za mu kashe ka ba.’

26. Sai ka ce musu, ‘Na roƙi sarki da ladabi don kada ya mai da ni a gidan Jonatan, don kada in mutu a can.’ ”

27. Dukan sarakuna suka tafi wurin Irmiya suka tambaye shi. Shi kuwa ya amsa musu yadda sarki ya umarce shi. Sai suka daina magana da shi, tun da yake ba wanda ya ji maganar da ya yi da sarki.

28. Irmiya kuwa ya yi zamansa a gidan waƙafi har ranar da aka ci Urushalima da yaƙi.

Karanta cikakken babi Irm 38