Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 37:8-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Kaldiyawa kuwa za su komo su yi yaƙi da wannan birni. Za su ci birnin, su ƙone shi da wuta.

9. Ni Ubangiji, na ce kada ku ruɗi kanku da cewa Kaldiyawa ba za su dawo ba, gama ba shakka za su zo.

10. Ko da a ce za ku ci dukan rundunar sojojin Kaldiyawa wadda take yaƙi da ku, sauran waɗanda kuka yi wa rauni da suke kwance a alfarwai za su tashi su ƙone birnin da wuta.’ ”

11. Da rundunar sojojin Kaldiyawa ta janye daga Urushalima saboda zuwan rundunar sojojin Fir'auna,

12. sai Irmiya ya tashi daga Urushalima zai tafi can ƙasar Biliyaminu, don ya karɓi nasa rabo tare da dangi.

13. A sa'ad da ya isa Ƙofar Biliyaminu, shugaban matsara, Irija ɗan Shelemiya, ɗan Hananiya, ya kama annabi Irmiya ya ce, “Kai kana gudu zuwa wurin Kaldiyawa ne.”

Karanta cikakken babi Irm 37