Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 36:25-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Ko da yake Elnatan, da Delaiya, da Gemariya, sun faɗa wa sarki kada ya ƙone littafin, amma ya yi biris da su.

26. Sarki ya umarci Yerameyel ɗan sarki, da Seraiya ɗan Azriyel da Shelemiya ɗan Abdeyel, su kamo Baruk magatakarda da annabi Irmiya, amma Ubangiji ya ɓoye su!

27. Bayan da sarki ya ƙone littafin da Baruk ya rubuta ta wurin shibtar da Irmiya ya yi masa, sai Ubangiji ya yi wa Irmiya magana, ya ce,

28. ya ɗauki wata takarda ya rubuta dukan maganar da take cikin littafin da Yehoyakim Sarkin Yahuza, ya ƙone.

29. Zai kuma ce wa Yehoyakim Sarkin Yahuza, “Haka Ubangiji ya ce maka, ka ƙone littafin, kana cewa, ‘Don me ka rubuta a cikinsa, cewa lalle Sarkin Babila zai zo ya hallaka wannan ƙasa, zai kashe mutum duk da dabba?’

30. Saboda haka Ubangiji ya ce Yehoyakim, Sarkin Yahuza, ba zai sami magāji wanda zai zauna a gadon sarautar Dawuda ba. Za a jefar da gawarsa a waje ta sha zafin rana, da dare kuma za ta sha matsanancin sanyi.

31. Zan hukunta shi, shi da zuriyarsa, da barorinsa saboda muguntarsu. Zan kawo dukan masifar da na hurta a kansu, da a kan mazaunan Urushalima, da a kan mutanen Yahuza, amma sun ƙi ji.”

32. Sai Irmiya ya ɗauko wata takarda ya ba Baruk, magatakarda, ɗan Neriya. Shi kuwa ta wurin shibtar Irmiya, ya rubuta dukan maganar da take a wancan littafi, wanda Yehoyakim Sarkin Yahuza ya ƙone a wuta. An ƙara magana da yawa kamar ta dā.

Karanta cikakken babi Irm 36